IQNA

Jerin Gwanon Adawa Da Kudirin Trump A Majami’ar Haward

22:53 - October 18, 2017
Lambar Labari: 3482013
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin daliban jami’a a birnin Cambridge da ke cikin jahar Massachusetts a kasar Amurka, sun yi gangamin yin Allah wadai da matakan Trump na takura ma msulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na thecrimson cewa, a jiya wasu daga cikin daliban jami’ar Haward a birnin Cambridge na Amurka, sun yi gangamin yin Allah wadai da matakan Trump na takura ma msulmi tare da yin kira da a taka ma Trump birki a kan wannan bakar akida tasa.

Masu gangamin sun gayyaci wasu daga cikin abokansu msuulmi domin shiga gangami, a loacin da ake yin gangamin a musulmi sun yi sallolin magriba da Isha’ia kan matattakalun majami’ar, yayin da sauran dalibai kiristoci suke basu kariya.

Anwar Omish daya ne daga cikin dalibai musulmi da suka halarci wannan gangami da dalibai kiristoci suka shirya domin nuan goyon baya ga msuulmin Amurka, inda ya bayyana cewa hakika wannan babban ci gaba ne wanda duniya take gani, kuma darasi ne ga sauran al’umomi.

Ya ci gaba da cewa babban abin bakin ciki ne yadda shugaban Amurka ya shelanta kiyayya da addinin muslunci a hukumance, ta yadda zai yi mu’amala da wasu kasashen msulmi ne kawai saboda maslaharsa ta kudi kawai.

Tun kafin ya dare kan kujerar shugabancin Amurka, Trump ya yi alkawalin cewa zai shiga kafar wando daya da musulmi, inda bayan hawansa ya saka kasashen musulmi 6 a cikin kasashen da ya haramtawa shiga Amurka.

3654121


captcha