IQNA

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Gangamin La'antar Trump A Duniya

16:55 - December 11, 2017
Lambar Labari: 3482190
Ana ci gaba da gudanar da gangami da jerin gwanoa kasashen duniya la'antar shugaban kasar Amurka a kan kudirinsa na amincewa da birnin Quds a matsayin birnin yahudawa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, Musulmi mazauna kasashen turai da suka hada da Birtaniya, Jamus, Holland, Sweden, Canada, Amurka da sauransu, suna ci gaba da gudanar da jerin gwano da gangami, domin nuna rashin amincewa da matakin Donald Trump na shelanta birnin Quds a matsayin fadar mulkin yahudawan Isra'ila.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da haramtacciyar kasar Isra'ila take ci gaba da kara mamaye yankunan Palastinawa tare da gina matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump dais hi ne shugaban kasar Amurka na farko da ya amince da wannan kudiri , tun bayan da majalisar dokokin Amurka ta sanya hannun a kansa shekaru fiye da ashirin da suka gabata.

Kasashen duniya da suka hada har da manyan kawayen Amurka duk sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan mataki, kamar yadda majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyar turai, duk sun nuna rashin yardarsu da wanann mataki.

3671091

 

 

 

captcha