IQNA

Bayan Harin New Zealand An Kai Wa Musulmi Wani Harin A London

23:09 - March 16, 2019
Lambar Labari: 3483466
Kasa da sa'oi ashirin da hudu da kai harin kasar New Zealanda kan musulmi, an kai wani harin a kan wani musulmi a birnin London na kasar Birtaniya.

Jaridar Indepent ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, a jiya Juma'a kasa da sa'oi 24 da kai harin da aka yi a kan masallacin musulmia  kasar New Zealand, wasu masu kyamar muslunci a birnin London na kasar Birtaniya sun kai farmaki da wukake a kan wani musulmi a  lokacin da yake fitowa daga cikin wani masallacia  birnin na Londin.

Rahoton ya ce mutane wasu ne uku daga cikin masu tsatsauran ra'ayin kin jinin musulmi a kasar ta Birtaniya suka kai harin a lokacin da aka kammala salla a cikin wani masallaci, inda suka biyu daga cikinsu suka nufi wani musulmi a lokacin da ya fito daga cikin masallacin suka yanke shi da wuka, inda suka yi masa munanan raunuka.

kafin zuwan jami'an tsaroa  wurin mutanen sun tsere, kuma babu wani wanda aka kama daga cikinsu, amma jami'an 'yan sandan London sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin.

3798102

 

 

 

 

 

 

captcha