IQNA

Kotun Isra’ila Ta Bayar Da Umarnin Rufe Masallacin Bab Al-Rahma

23:44 - March 18, 2019
Lambar Labari: 3483469
Daya daga cikin mambobin kwamitin kula da masallacin Quds Hatam Abdulkadir ya bayyana cewa ba su amince da hukuncin kotun Isra’ila kan rufe masallacin Bab Rahma ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na jaridar Dunyal Watan a Palastine ya bayar da rahoton cewa, a jiya wata kotun Isra’ila da ke birnin Quds ta yanke hukuncin cewa dole ne a  rufe masallacin Babu Rahma da ke gefen masallacin Aqsa.

Hatam Abdulkadir ya ce kotun Isra’ila ba ta da hurumin tsoma baki dangane da abin da ya shafi masallacin Aqsa da kewaye, domin kuwa wuri ne na ibada mallakin musulmi.

A kan haka ya ce za su kalubalanci wannan mataki, domin kuwa hakan lamari mai hadari matukar dai har kotun Isra’ila za ta iya yanke hukuncin rufe daya daga cikin masallatai na musulmi masu tarihi.

Kotun Isra’ila ta baiwa kwamitin da ke kula da masallacin Quds wa’adin kwanaki 60 na daukaka kara, idan kuma wa’adin ya shige to kuwa kotun za ta bayar da umarni ga jami’an tsaro da su rufe masallacin.

Masallacin Babu Rahma dai masallaci ne da ke gefen masallacin Quds, wanda yake da tarihi a cikin musulunci, wanda kuma Isra’ila ta rufe a lokutan baya, amma a cikin ‘yan makonni da suka gabata musulmi Falastinawa suka sake bude masallacin, kuma suka ci gaba da yin salloli a  cikinsa.

3798612

 

 

captcha