IQNA

Amnesty Int. Ta Bukaci Da Hukunta Jagororin Kungiyoyi Masu Kyamar Musulmi

23:49 - March 18, 2019
Lambar Labari: 3483471
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci a kame tare da hukunta dukkanin shugabannin kungiyoyi masu nuna kyama a ga musulmi a  duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Aljazeeranet ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a jiya, kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci gwamnatocin kasashen duniya da su dauki matakin hukunta jagororin kungiyoyi masu nuna kyama ga musulmi a  kasashensu.

Bayanin ya ce nuna adawa da kyama ga musulmi a wasu kasashen duniya yana da alaka ne da batutuwa na siyasa, amma a halin yanzu lamarin yana neman ya zama wata akida a tsakanin masu dauke da irin wannan tunani a wasu kasashe na duniya.

Dangane da harin da aka kaiwa musulmi birnin Christ Church na kasar New Zealand kuwa, bayanin na Amnesty International ya ce wannan yana daga cikin alamu na yadda wannan lamari na kyamar musulmi yake kara tsananta da kuam yaduwa a wasu kasashen dab a a san hakan ba, wanda kuma ke kara tabbatar da wajabcin daukar matakai na tunkarar lamarin a duniya.

3798719

 

captcha