IQNA

Jagora Ya Bukaci Mayar Da Hankali Ga Ayyukan Bunkasa Tattalin Arziki Cikin Gida

23:55 - March 21, 2019
Lambar Labari: 3483478
Jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin mayar da hankali ga ayyukan bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar ta Iran daga cikin gida.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran ya bayyana hakan ne a cikin sakon da ya aike na taya al’ummar kasar Iran murnar shiga sabuwar shekarar hijira Shamsiyya, wadda ta fara daga yau Alhamis.

Da farko dai jagoran ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar lokacin haihuwar Amirul muminin Ali dan Abu Talib (AS). Bayan haka kuma ya bayyana shekarar Shamsiyya da ta kare a jiya da cewa, shekara ce wadda ta kasance cike da kalu bale ga al’ummar Iran, da hakan ya hada da matsin lamba daga dukkanin bangarori a  kan kasar.

Wannan matsin lamba kuwa ya hada da na siyasa da tattalin arziki, tare da kokarin mayar da kasar saniyar ware a yankin, ya ce amma duk da hakan, himma da juriya da imani na al’ummar kasar, sun sanya makiya ba su iya cimma burinsu ba, domin kuwa a ranar tunawa da cikar shekaru arba’in da samun nasarar juyin juya halin muslucnia  kasar, al’umma sun tabbatar da hakan.

Jagora ya ci gaba da cewa, dangane da tasirin matsin matsin lamba da takunkumai na Amurka da kasashen yammacin turai a kan Iran kuwa, akwai matakai da dama da ya kamata a dauka da za su taimaka wajen karya lagon manufar makiya ta wannan fuska, daga ciki kuwa har da kara karfafa ayyukan masana’antu da kamfanoni na cikin gida, da kara samar da guraben ayyukan yi, wanda kuma ya zama wajibi a cikin wannan shekara a ga tasirin wadannan matakai a cikin kasar.

Ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata, al’ummar kasar sun nuna himma matuka wajen mayar da hankali a kan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, fiye da dogaro da abubuwan da ake samarwa a kasashen ketare, wanda hakan ma yana babban tasiri wajen dakushe yunkirin makiya kasar na gurgunbta tattalin arzikinta da ayyukan masana’antu da kamfanonin kasar.

Daga karshe kuma ya kara jaddada kira a kan gwamnatin kasar da ta kara bada himma wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta wajen yi wa al’umma hidima, da kuma sauraren koke-kokensu, da hanzarta aiwatar da dukaknin sabbin tsare-tsare shirye-shirye na tattalin arziki, tare da yin fatar ganin cewa a cikin wannan shekara an iya aiwatar da abubuwan da tsara domin ci gaban kasar a dukkanin bangarori.

 

3799238

 

 

captcha