IQNA

MDD Ta Bukaci A Kawo Karshen Rikicin Libya Cikin Gaggawa

23:59 - May 24, 2019
Lambar Labari: 3483670
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta bukaci da a kawo karshen rikicin kasar Libya cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, majalisar dinkin duniya ta bukaci da a kawo karshen rikicin kasar Libya cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba, domin ganin an kubutar da fararen hula.

shi kuma a nasa bagaren shugaban gwamnatin hadin kasar kasar Libiya Fa'iz Siraj a gefen taron birnin Tunus na cewa abinda yake faruwa a kasarsa,rikici ne tsakanin gwamnatin farar hula da gwamnatin soja, domin bukatarsu shi ne dawo da kama karya a kasar Libiya.

Ya tabbatar da cewa bukatar sauyi na siyasa hakki ne na ko wani dan kasar Libiya, to saidai neman wannan bukata dole ne abin ta hanyar doka.

Har ila yau shugaban gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya ya nanata cewa har yanzu akwai lokaci na dakatar da zubar da jini a kasar, a kuma koma kan tebirin tattaunawa domin magance sabanin dake tsakanin bangarorin biyu.

A bangare guda kuma, ministan cikin gidan kasar ta libiya Fathi Bashagha ya bukaci dakarun tsaron kasar karkashin jagorancin khalifa haftar janyewa daga birnin Tripoli.

3814253

 

 

captcha