Kamfanin dillancin labaran iqna, daya daga cikin fitattun jaridu a tarayyar Najeriya mai suna Peoles Daily ta buga wata makala dangane da ranar Quds ta duniya da a ke gudanarwa a karshen watan azumi.
A cikin makamalr an yi siahara da cewa wannan rana marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya kafa jamhuriyar musulunci ta Iran, shi ne ya assasa ta.
A okwace ranar Juma'a ta karshen watan azumi na kowace sekara ana gudanar da jerin gwanon ranar quds a sassa daban-daban na duniya, domin nuna goyon baya ga al'ummar palastine.
Haka nan kuma a cikin makalar an yi ishara da cewa, baya ga musulmi hata wawadanda ba musulmi wadanda suke son ganin adalci ya tabbata a duniya, sukan shiga cikin wannan jerin gwano domin bayyana ra'ayinsu.