IQNA

An Yi Kira Zuwa Ga Bore A Palastine Kan yarjejeniyar Karni

23:50 - June 10, 2019
Lambar Labari: 3483726
Bangaren kasa da kasa, an yi kira da a shiga bore a yankunan palastine domin bijirewa abin da ake kira da yarjejeniyar karni.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shafin yada labarai na JNS ya ayar da rahoton cewa, kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa sun yi kira da a yi kira da a shiga bore a yankunan palastine domin bijirewa abin da ake kira da yarjejeniyar karni.

Dukkanin kungiyoyin Falastinawa bakinsu ya zo daya wajen yin kira da a kaurace wa abin da ake kira da yarjejeniyar karni, wadda suke kallonta  a matsayin wata dasisa da nufin ci gaba da mamaye yankunansu da kuma tabbatarsu karkashin Isra'ila.

Tun kafin wannan lokacin gwamnatin kwarya-kwaryan ci gishin kai ta Falastinawa ta sanar da cewa ba za ta amince da abin da ke cikin yarjejeniyar karni ba, kamar yadda kuma jami'anta ba za su halarci taron da za a gudanar a Bahrain ba.

Kasashen Amurka da Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa gami da Isra'ila ne suka kirkiro abin da ake kira da yarjejeniyar karni, wadda za ta tabbatar da ikon Isra'ila a kan falastinawa, da kuma amincewa da birnin quds a matsayin fadar mulkin Isra'ila.

 

http://iqna.ir/fa/news/3818288

captcha