IQNA

Jami’an Tsaron Faransa Sun Cafke Wasu Mutane Da Ke Shirin Kaiwa Musulmi Da Yahudawa Hari

23:57 - June 11, 2019
Lambar Labari: 3483729
Bangaren kasa da kasa, jamian tsaron kasar Faransa sun damke wasu mutane da ke shirin kaddamar da hare-hare a kan wuraren ibadar musulmi da na yahudawa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Yabladi ya bayar da rahoton cewa, a yau Talata jami’an tsaron kasar ta Faransa sun sanar da cewa, sun samu nasarar cafke wasu gungun mutane da ke shirin kaddamar da hare-hare a kan wuraren ibadar musulmi da na yahudawa a sassa d kasarban-daban na Faransa.

 Bayanin ya ce dukkanin mutanen mambobi na wata kungiya ne da ake kira Balack Birds mai tsatsauran ra’ayin kin jinin mabiya addinai a kasar.

Yanzu haka dukkanin mutanen da aka kame ana tsare da su, kuma tuni bangaren shari’a a kasar Faransa ya fara gudanar da bincike kan lamarinsu.

Majiyoyin shari’a  a kasar sun ce ga dukkanin alamu mutanen suna shirin kaddamar da wasu munanan hare-hare ne na kisan gilla a kan musulmi da kuma yahudawa mazauna kasar ta Faransa.

 

3818686

 

captcha