IQNA

Ganawar Shugaba Rauhani Da Firayi Ministan Japan

23:53 - June 13, 2019
Lambar Labari: 3483733
A jiya ne Firayi ministan kasar Japan Shinzo Abe ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Iran, inda yake ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, bayan isowar birnin Tehran dai a jiya Laraba, ya fara ganawa ne da shugaban kasar ta Iran Hassan rauhani, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa daban-daban, da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma wadanda suka shafi siyasar kasa da kasa da yankin gabas ta tsakiya.

Bayan kammala tattaunawarsu shugaba Rauhani da Shinzo Abe sun gudanar ad taron manema labarai a daren jiya, inda shugaba Rauhani ya bayyana cewa tattauna batutuwa suka shafi irin rawar da Japan za ta iya takawa wajen daidaituwar lamurra a yankin gabas ta tsakiya.

Rauhani ya ce ya sheda wa Firayi ministan na Japan cewa, irin matakan da gwamnatin Amurka mai ci a yanzu take dauka a kan kasar Iran, suna kan gaba wajen kara sanya lamurra su dagule a yankin, musamman yadda Amurka take yin gaban kanta wajen yin hawan kawara a kan dokokoki da ka’idoji da kuma yin fatali da yarjeniyoyi na kasa.

Rauhani ya ce Iran ba ta da niyyar shiga yaki da wata kasa, amma kuma zata mayar da martani da zai girgiza duk wata kasa da ta yi gigin yin shishigi a kanta.

A nasa bangaren Firayi ministan kasar ta Japan Shinzo Abe ya bayyana cewa, zuwa tasa a Iran tana da matukar muhimmanci, domin ba komai za ta kara taimakawa wajen warware matsaloli da dama, wadanda za su iya shafar yankin baki daya.

Kamar yadda ya ce sun yaba da yadda Iran take yin aiki da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da ita, kamar yadda kuma yake fatan Iran za ta ci gaba da yin hakan.

Duk da cewa bayanai sun yi fitowa kan cewa babbar manufar ziyarar Firayi ministan kasar at Japan a Iran ita ce shiga tsakani a takaddamar da ta kunno kai tsakanin Iran da Amurka, amma bangarorin biyu ba su tabo wani batu kan hakan ba a gaban manema labarai.

Rauhani da Abe, sun tattauna kan batun shirin kasar Japan na saka hannun jari a cibiyar ayyukan iskar gas da ke kudancin Iran, da kuma tashar jiragen ruwa ta Chabhar ta kasar Iran, da kuma batun hada-hadar kudade a tsakanin kasashen biyu, da kuma bunkasa sauran harkoki na diflomasiyya tsakanin kasashen na Iran da Japan.

 

3819046

 

 

 

captcha