IQNA

Ayatollah Sistani Ya Yi Gargadi Kan Yiwuwar sake Dawowar Daesh

23:55 - June 14, 2019
Lambar Labari: 3483737
Babban malamin addini na kasar Irai ya yi gargadi kan yiwuwar sake dawowar ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh a kasar a nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Furat News ya bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da ya fitar a daidai lokacin da aka cika sekaru biyar da shelanta yaki kan ‘yan ta’addan Daesh, Ayatollah Sayyid Ali Sidtani ya yi gargadi cewa, ‘yan ta’addan za su iya dawowa a kowane lokaci.

Babban limamin Juma’a na Karbala Sayyid Ahmad Al-safi ne ya karanta jawabin, wanda a cikinsa Ayatollah Sistani ya jinjinawa al’ummar raki, dangane da irin jarunta da suka nuna wajen kare kasarsu daga ‘yan ta’adda da suka nemi wargaza kasar.

A ranar 13 ga watan Yunin 2014 ne Ayatollah Sistani ya bayar da fatawar wajabcin daukar makami domin yaki da ‘ta’addan daesh da suka shigo kasar da nufin mamaye ta, domin kafa abin da suke kir daular khalifanci.

Bisa wannan fatawa miliyoyin Irakawa ne musamman matasa suka shiga aikin soji na sa-kai domin kare kasarsu, inda suka fatattkin yakan ‘yan ta’addan da suka mamaye wasu yankunan kasar suna yada barna da sunan addini.

‘Yan ta’addan Daesh da suka fito daga kasashen duniya daban-daban- sun shiga cikin kasar Iraki nea  cikin shekara ta 2014, tare da taimakon wasu kasashen larabawa da suke adawa da gwamnatin kasar Iraki da al’ummarta, saboda dalilai na siyasa da kuma bangaranci na akida da banbancin mazhaba.

 

3819247

 

 

 

captcha