IQNA

Gudanar Da Taron Maulidin Imam Hassan Askari (AS) A Ankara

16:55 - January 21, 2016
Lambar Labari: 3480064
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da tarukan maulidin Imam Hassan Askari (AS) a birnin Ankara.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo karamin ofishin jakadancin kasar Iran a birnin Ankara cewa, an gudanar da taron maulidin Imam Hassan Askari (AS) tare da halartar daruruwan muminai.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da jawabi a tsakanin sallolin Magrib da isha, dangane da wannan rana mai albarka ta haihuwar daya daga cikin limaman shiriya mai tsarki.

Mabiya tafarkin Ahlul bait (AS) daga koina cikin birnin sun isa wurin domin halartar wannan taro mai albarka.

3469121

captcha