Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin libyaschannel.com cewa, a jiya aka kammala gasar hardar kur’ani a birnin Darul Baida wadda yara ‘yan kasa da shekaru 10 suka gudanar.
Bayanin ya ce yara mahardata yan kasa ad shekaru 220 maza da mata ne suka gudanar da gasar tsawon kwanaki goma, kuma sun fito ne daga cibiyoyin 60 na koyar da ur’ani a sassa na kasar.
Maikatar kula da harkokin addini ta kasar ce reshen Darul Baida ta dauki nauyin shirya gasar, wadda za a sanar da saamakonta ‘yan kwanaki masu zuwa.