IQNA

​WHO: Kasashen Afirka Su Dauki Kwararan Matakai Na Kariya Kafin Bude Iyakokinsu

23:57 - July 04, 2020
Lambar Labari: 3484952
Tehran (IQNA) Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci gwamnatocin kasashen Afrika da su dauki kwararen matakan kariya daga annobar coronavirus a daidai lokacin da suke shirin sake bude kan iyakokinsu don ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama.

Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Kawo yanzu kasashen Kamaru da Tanzania da Equitorial Guinea da Zambia sun fara jigilar fasinjojin jiragen sama, yayin da ake sa ran mambobin kasashen Kungiyar Yammacin Afrika 15 za su bude nasu iyakokin na sama nan da ranar 21 ga watan Yuli.

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya shiyar Afrika, Matshidiso Moeti ta ce; zirga-zirgar jiragen sama na da muhimmanci ga tattalin arzikin kasashe, amma akwai bukatar tsaurara matakai domin hana bazuwar cutar ta corona.

Hukumar Lafiyar ta Duniya ta shawarci kasashen da su tantance yanayin halin da ake ciki domin sanin ko ci gaba da takaita zirga-zirgar ya fi muhimmanci fiye da sake bude kan iyakokin.

Kazalika Hukumar ta WHO ta ce; abu ne mai matukar muhimmanci a tantance tsarin lafiyar kasashen na Afrika kan cewa ko yana da karfin tunkarar matsalar dauko cutar daga wata kasa, ko kuma suna da ingantaccen tsarin bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar tare da sanya ido a kansu.

ha.abna24.com

captcha