IQNA

Rauhani: A Mako Mai Zuwa Ne Za Sanar Da Bayani Kan Tarukan Muharram

21:12 - August 01, 2020
Lambar Labari: 3485041
Tehran: shugaba Rauhani na Iran ya bayyana cewa, a cikin mako mai zuwa ne za a sanar da yadda tarukan watan Muharram za su kasance.

A lokacin da yake zantawa da jami’an kiwon lafiya a bangaren cutar corona a yau, shugaba Rauhani na Iran ya bayyana cewa, bisa la’akari da irin yanayin da ake ciki a mako mai zuwa za a sanar da yadda tarukan watan Muharram za su kasance domin jama’a su zama suna da masaniya.

Ya ce ko shakka babu, jami’an kiwon lafiya musamman kwamitin yaki da corona corona sun taka rawar gani, ta yadda suka sadaukar da rayukansu da lokutansu da komai nasu domin yin taimako ga al’umma, duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta.

Dangane da jama’a kuwa, shugabay abyyana cewa, dole a kiyaye kaidoji da jami’an kiwon lafiya suka ginadaya, matukar dai ana son ganin samun ci gaba a kokarin da ake na ganin bayan wannan cuta a fadin kasar.

Abin da ya danganci tarukan wata mai zuwa kuwa, ya bayyana cewa akwai wasu tsare-tsare da ake da su, wadanda jami’an kiwon lafiya za su bayar, kuma daga mako mai zuwa za a sanar da abin da ya kamata yi.

Daga karshe kuma ya jinjin wa jagoran juyi kan bayanin da ya gabatarwa al’umma dangane da wajabcin kare kai da kuma daukar matakan kariya a kowane lokaci, domin ganin an yi aiki tare domin dakile wannan cuta.

 

3913895

 

 

 

captcha