IQNA

Wani Limami A Ghana Ya Yi Kira Da Kasashen Musulmi Su Karbi Ragamar Lamurran Hajji

21:16 - August 02, 2020
Lambar Labari: 3485045
Tehran (IQNA) daya daga cikin limaman musulmi a kasar Ghana ya bayyana cewa lamarin aikin hajji ya shafi dukkanin musulmi ne ba wata kasa guda daya ba.

A cikin wata zantawa da ta gudana a gidan radiyon Latino na kasar Ghana kan batun aikin hajji, Ibrahim manshah daya daga cikin limaman musulmi a kasar Ghana ya bayyana cewa, lamarin aikin hajji ya shafi dukkanin musulmi ne saboda haka ya kamata kasashen musulmi su karbi ragamar aikin hajji na kowace shekara.

Ya ce kamata ya yi a kafa wani kwamiti wanda zai kunshi mambobi daga dukkanin kasashen musulmi, wadanda za su rika fayyace abin da ya kamata a yi dangane da aikin hajji, domin kuwa harami ka’abah da masallacin manzo mallakin dukkanin musulmin duniya ne.

Haka nan kuma ya caccaki mahukuntan masarautar Al Saud, kan abin da ya kira mayar da sha’anin hajji da umara tamkar gadon gidansu, tare da saka siyasa a cikin lamarin, wanda kuma hakan ya yi hannun riga da koyarwa ta addini.

Malamin ya ci gaba da cewa, tun kafin wannan lokacin akwai kasashen mulmin da suka yi kira da a kafa irin wannan kwamiti, amma masarautar Al Saud ta yi biris ta batun, wanda kuma hakan shi ne maslaha a cewarsa.

 

3914159

 

 

captcha