IQNA

Kwararan Matakai A Wuraren Ibada A Wasu Jihohin Najeriya

21:28 - August 03, 2020
Lambar Labari: 3485050
Tehran (IQNA) wasu daga cikin jiohin Najeriya sun sanar da daukar kwararn matakai a wuraren ibada da suka hada da masallatai da majami’oi.

Shafin yada labarai na Peace FM Online ya bayar da rahoton cewa, gwamnan jihar Lagos gari mafi yawan jama’a a kudancin Najeriya ya sanar da cewa, za a bude wuraren ibada amma bisa sharadin cewa za  akiyaye ka’idoji na kiwon lafiya.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da cewa, za a bude masallatan Juma’a a ranar Juma’a mai zuwa, amma bisa sharadin cewa dole ne a kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya, da hakan ya hada da yin feshi a masallatai, da kuma saka takunkumin fuska gami da bayar da tazara.

Haka nan kuma ya bayyana cewa,a  ranar Lahadi mai zuwa, majami’oin mabiya addinin kirista za su iya budewa domin ibada, amma tare da sharuddan da ya ambata.

Baya ga haka kuma ya ce tsoffi wadanda shekarunsu suka haura 65 babu bukatar su halarci wuraren ibada.

 

3914333

 

 

 

 

 

 

captcha