IQNA

An Fara Daukar Matakan Da Suka Dace Domin Tunkarar Sabuwar Cutar Corona A Afirka Ta Kudu

15:35 - November 28, 2021
Lambar Labari: 3486614
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta sanar da cewa, ta fara daukar matakan da suka dace domin tunkarar sabuwar cutar corona da ta bullo.
Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ce ta fara daukar matakan kiwon lafiya a kasar don kaucewa yaduwar sabon nau’in cutar Covid 19 wanda aka gano a kasar, wanda kuma yake saurin yaduwa cikin mutane.
 
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa news’ ya nakalto ministan kiwon lafiya na kasar Afrika ta Kudu Joe Phaahla yana cewa a cikin ‘yan kwanaki 4-5 da suka gabata yawan wadanda suke kamuwa da cutar ya karu musamman a lardun Gauteng da Limpopo.
 
Amma idan muatne sun kiyaye matakan kiwon lafiya sannan suka yi alluran riga kafin cutar ana iya shawo kan sabon cutar da Covid 19 da ta bullo a kasar.
 
‘Yan kasar da dama, daga ciki har wadanda suka yi cikekken allurab riga kafin cutar suna jin tsaron mai yuwa su kamu da iya don likitoci sun ce mai yiwa ragakafin da aka yiwa mutane ba zai karesu daga kamuwa da it aba don karfin da take da shi da saurin yaduwa.
 
Ya zuwa yanzun kasashen duniya da dama sun hana duk wadanda ya fito daga kasar Afirka da kudu da makobtanta shigowa kasashensu. Daga ciki har da Amurka, Burtaniya
 

 

4016734

 

captcha