IQNA

An bude taron kur'ani na kasa da kasa a Karbala

17:48 - January 18, 2022
Lambar Labari: 3486836
Tehran (IQNA) cibiyar Darul kur'ani karkashin hubbaren Imam Hussain ta sanar da gudanar da taron kur'ani na kasa da kasa, wanda shi ne irinsa na farko.
An bude taron kur'ani na kasa da kasa a Karbala

Cibiyar Dar Al-Qur'ani ta hubbaren Imam Hussain (AS)  ta sanar da gudanar da taron kur'ani na kasa da kasa karo na farko don hadawa da daidaita ka'idojin shari'a kan gasar kur'ani ta 'yan mata.

An gudanar da taron ne a dakin taro na Umm Abiha da ke Jami'ar Zahra tare da halartar wakilai daga kasashe 16.

Dr. Sheikh Khair al-Din al-Hadi, shugaban Darul-Qur'an a jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ya ce: "kaunar kur'ani mai tsarki da duk wani abu da ya shafi harkar kur'ani a cikin addinin Musulunci, na daya daga cikin muhimman abubuwan da suke nuna takawa."

Ya kara da cewa: Wannan taro na musamman wanda shi ne irinsa na farko zai zama wani muhimmin taro ga cibiyoyin kur'ani mai tsarki domin tsara mahanga da shirye-shiryen da aka gabatar a wannan taro.

Al-Hadi ya ce, a daya bangaren kuma, wannan taro zai haifar da daidaito da da'a a cikin sharuddan yanke hukunci a gasar kur'ani mai tsarki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4029358

captcha