IQNA

Gwamnatin San'a Ta Dora Alhakin Kisan Kiyashin Kawancen Saudiyya A Yemen A kan Amurka

21:22 - January 18, 2022
Lambar Labari: 3486837
Tehran (IQNA) gwamnatin San'a ta dora alhakin kisan kiyashin da kawancen Saudiyya ke yi a Yemen a kan gwamnatin Amurka.

Tashar Almasira ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar kare hakkin bil'adama ta kasar Yemen ta yi Allah-wadai da hare-haren da  kawancen Saudiyya ya kai a yankin Al-Hai al-Libi da ke arewacin birnin Sana'a babban birnin kasar Yemen.

Ma'aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, "kai hare-hare a kan gidajen 'yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba laifi ne na yaki, wanda gwamnatin Al-Saud da Hadaddiyar Daular Larabawa suke tafkawa wadanda suka keta ka'idoji na kasa da kasa da kuma keta hakkin bil adama,a  cewar sanawar.

Ma'aikatar kare hakkin bil-Adama ta kasar Yemen ta jaddada cewa, laifukan da kawancen Saudiyya suka aikata kan al'ummar kasar Yemen, ana aiwatar da su ne tare da goyon bayan gwamnatin Amurka da kuma makaman Amurka tare da hadin gwiwar kasashen duniya.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da dakarun kawancen Saudiyya da Amurka suka kai a daren Litinin a lardin Sanaa ya kai 12 da jikkata wasu 11, wasu daga cikinsu mata da kananan yara.

Yayin da wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su na karkashin baraguzan ginin, kuma ana ci gaba da aikin ceto, majiyoyin Yemen sun ce adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

A daren jiya kuma sau biyu dakarun kawancen Saudiyya suna kai hari a harabar majalisar dokokin da ke titin Al-Satin ta Yamma da kuma makarantar horas da sojoji da ke Sanaa babban birnin kasar.

 

4029444

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya amurka
captcha