IQNA

Likitocin Kasa Da Kasa: Saudiyya Ta Kashe Fararen Hula Saba'in A Yau A Kasar Yemen

18:23 - January 21, 2022
Lambar Labari: 3486848
Tehran (IQNA) kungiyar likitocin kasa da kasa ta sanar da cewa, fararen hula akalla 70 ne suka rasa rayukansu a yau a kasar Yemen sakamakon hare-haren da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kansu.

A yau Juma'a kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa mutane 70 ne suka mutu tare da jikkata wasu 138 a wani hari da jirajen yakin Saudiyya suka  a wani gidan yari da ke birnin Saada da ke arewacin kasar Yemen.

Ita ma Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa a Yemen ta sanar a baya cewa ta kirga sama da mutane dari da suka mutu da kuma jikkata bayan wani hari da aka kai a wani gidan yari a Saada da ke arewacin kasar Yemen a yau Juma'a.

Kakakin kungiyar agaji ta Red Cross a Yemen, Bashir Omar, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an kashe mutane fiye da 100 ko kuma suka jikkata bayan harin da aka kai a wata cibiyar tsare mutane da ke Saada, yana mai cewa "lambobin na karuwa."

Kuma hukumar 'Agence France Presse' ta nunar da cewa kungiyar Houthi "Ansar Allah" ta zargi kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya da kaddamar da harin a gidan yarin.

Wannan karuwar hare-haren kawancen na Saudiyya kan Yemen ta zo dai-dai da kalaman sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, game da yadda ake ci gaba da kai hare-hare ta sama a Sanaa, Hodeidah da sauran wurare a kasar Yaman cikin ‘yan kwanakin nan.

 

4030137

 

 

 

captcha