IQNA

An dakatar da ayyukan cibiyoyin kur'ani na Aljeriya na tsawon kwanaki 10 domin yaki da cutar Corona

20:00 - January 21, 2022
Lambar Labari: 3486849
Tehran (IQNA) An dakatar da makarantun kur'ani na Aljeriya da dakunan karatu da tarukan kur'ani a kasar ta Aljeriya na tsawon kwanaki 10 domin dakile barkewar cutar korona.

Shafin yada labarai na Al-shuruq ya bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar da ke kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayar da umarnin dakatar da karatu na tsawon kwanaki 10 a makarantun kur'ani da dakunan karatu da kuma tarurrukan kur'ani na kasar domin yaki da cutar korona.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Bayan dakatar da cibiyoyin ilimi na Aljeriya na tsawon kwanaki 10 domin tunkarar barkewar cutar korona, har ila yau ma'aikatar kula da harkokin addini ta ta Aljeriya ta sanar da dakatar da karatun kur'ani a makarantun kur'ani da dakunan karatu na tsawon kwanaki 10 a dukkanin larduna.

Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta sanar da cewa: "An dauki wannan matakin ne daidai da shawarar da manyan jami'an kasar suka yanke na tunkarar annobar korona, kuma a cewarta, za a fara aiki da dokar ne daga jiya Alhamis.

 

4030200

 

captcha