IQNA

Kai Hari A Kan Tarukan Ashura Ci Gaban Yakin Kabilun Larabawa Ne Kan Manzon Allah

23:56 - October 06, 2016
Lambar Labari: 3480831
Bangaren kasa da kasa, Said Shahabi daya daga cikin jagororin gwagwarmayar siyasa a Bahrain ya bayyana harin da masarautar kasar ke kaiwa kan tarukan ashura da cewa harin kabilu larabawa ne kan manzon Allah (SAW) da ahlul bait (AS).
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Bahrain yaum cewa, Said Shahabi wanda daya ne daga cikin jagororin gwagwarmayar siyasa a Bahrain da ke zaune a birnin Landan, ya bayyana harin da masarautar kasar ke kaiwa kan tarukan ashura da cewa harin kabilu larabawa ne kan manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa.

Ya ci gaba da cewa babu wani lokaci wanda kabilun larabawa suka daina cutar da manzon Allah, kamar yadda kuma har yanzu suke ci gaba da yin hakan ta hanyoyin da suka sawaka gare su, daga ciki kuwa har da hana tarukan ashura a wasu kasashen da kabilun larabawa suke mulki kamar Bahrain.

Said Shahabi y ace bababn abin da masu mulki daga cikin larabawan kauye da ke mulkin wadannan kasashe suak ganewa shi ne, babu wani lokaci da yin amfani da karfi ya taba hana gaskiya bayyana, kuma raya lamarin manzon Allah da iyalan gidansa raya lamarin muslunci ne.

Kamar yadda kuma ita kanta ashura da abin da ya faru da Imam Hussain (AS) da sauran iyalan gidan amnzo a ranar, babban darasi ga dukkanin al’ummar musulmi baki daya kai har da sauran yan adam ma, domin kuwa mikewar da Imam Hussain (AS) ya yi, tana da alaka ne da neman tabbatar da adalci da zaman lafiya da ceto dan adam daga bautar bayi zuwa ga bautar ubangiji da yanci.

3535778

captcha