Kamfanin dillancin labaran iqna, hukumar rdaiyo da talabijin ta kasar Turkiya ta bayar ad rahton cewa, a jiya kungiyar jin kai ta kasar Turkiya TIKA ta raba abinci ga mabkata a kasar Gambia.
Isama'ila Safa Yugar jakadan kasar Turkiya a kasar Gambia ya harci wurin raba taimakon, wanda ya kai ton 8 na abinci, inda ya bayyana cewa kasarsa tana gudaar da irin wannan aiki a kasar Gambia tsawon shekaru masu yawa.
Imam Sharif Malik Badjan babban malamin addinin muslunci a kasar wanda shi ma ya halarci wurin, ya bayyana taimakon na Turkiya da cewa abin yabawa ne, musamman ganin cewa akwai mutane da dama masu azumi da suke bukatar irin wannan taimako a kasar.
Kafin wannan lokacin ma wannan cibiya ta kasar Turkiya, ta raba taimakon kayan abinci da wasu kayayykin bukata a gidajen kason kasar Gambia, kamar yadda ta bayar da wani taimakon ga marassa lafiya da suke kwancea asibitocin kasar.