IQNA

Za A Saka Wani Sisin Tsohon Zinariya Mai Rubutun Muslunci A Kasuwa A Landan

22:47 - October 05, 2020
Lambar Labari: 3485248
Tehra (IQNA) za a saka wani tshon sisin zinariya na tarihi da yake dauke da rubutun musulunci a kasuwa a birnin Landan.

Jaridar Art Daily ta bayar da rahoton cewa, ana shirin saka wani tshon sisin zinariya na tarihi da yake dauke da rubutun musulunci a kasuwa a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Wannan sisin zinariya dai tarihinsa na komawa ne ga daular Guriyan wadda ta hada yankunan India da kuma kudancin Asia,a  lokacin mulkin sarki Mu’izzuddin, kuma ana sa ran za a sayar da shi a kan kudi daga fan dubu 200 zuwa dubu 300.

Fadin wannan sisin zinariya dai zai kai ml 46, kamar yadda kuma nauyinsa zai kai gram 45, kuma zinariya ce zalla.

Kamfanin Morton & Eden ne zai dauki nauyin jagorantar cinikin wannan sisin zinariya mai tarihi.

An haifi sarki Mu’aizzuddin ne a garin Gur da ke cikin kasar Afghanistan a halin yanzu, tare da taimakon dan uwanda Giyasuddin sun kafa babbar daula da hada India da kudanci zuwa gabashin Asia, wadda ta hade da tekun Caspian.

 

3927296

 

 

captcha