IQNA

An Bude Taron Gasar Kur’ani Ta Kasa Baki Daya A Birnin San’a Na Kasar Yemen

9:24 - March 18, 2021
Lambar Labari: 3485751
Tehran (IQNA) an bude gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki a kasar Yemen a birnin San’a fadar mulkin kasar.

Shafin saba net ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne aka bude taron gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a Yemen a birnin San’a fadar mulkin kasar, wadda za ta dauki tsawon kwanaki 20 ana gudanarwa, tare da halartar mahardata kur’ani 200 dagga sassan kasar baki daya.

Hussain Maqbuli mataimakin firayi ministan gwamnatin San’a ya bayyana cewa, an fara gudanar da wannan gasa ne a daidai lokacin da ake cika shekaru goma sha bakawai da kisan Husaiin Badruddin Alhuthy.

Ya ce wannan bawan Allah ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafa samari masu Imani da juriya da kumajin kare kasarsu da al’ummarsu daga mamayar makiyan kasar Yemen.

A cewar mataimakin firayi ministan gwamnatin San’a, Amurka da Isra’ila tare da munafukai daga cikin sarakunan larabawa ne suke da hannu wajen kisansa shekaru sha bakawai da suka gabata, saboda ya zama karfen kafa da ya hana su cimma babaken manufofinsu a kan al’ummar Yemen.

Ya ci gaba da cewa, wannan gasar kur’ani tana a matsayin tunawa ce ga gwagwarmayarsa, a kan haka ne a kowace shekara a daidai wannan lokaci ake gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a birnin San’a domin tunawa da shi da kuma sadaukarwara.

3960047

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gasar kur’ani mai tsarki kasar yemen
captcha