IQNA

Kungiyar Hamas ta yaba da korar wakilan yahudawan sahyuniya daga taron kungiyar tarayyar Afrika

16:19 - February 19, 2023
Lambar Labari: 3488684
Tehran (IQNA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta yaba da matsayin kungiyar Tarayyar Afirka na goyon bayan al'ummar Palasdinu da kuma korar tawagar Isra'ila daga taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Jihad Taha, kakakin kungiyar Hamas, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, korar tawagar Isra'ila ta yi daidai da matsayi da kimar kungiyar Tarayyar Afirka a kodayaushe.

Ya kuma yi kira ga kasashen Afirka da su dauki irin wadannan matsayi masu kima da kuma mayar da gwamnatin sahyoniya saniyar ware gwargwadon iko.

Jami'an tsaro na taron Tarayyar Afirka sun kori tawagar Isra'ila da ke shirin halartar taron kolin kungiyar karo na 36 a Addis Ababa.

Tawagar Isra'ila ta yi ikirarin cewa tana da goron gayyata na halartar taron bude taron kungiyar Tarayyar Afirka, amma ba su iya tabbatar da hakan ba, sakamakon haka jami'an tsaron kasar sun kore su daga zauren taron da karfi.

Shafin yada labaran yahudanci na "Walla" ya jaddada cewa gwamnatin sahyoniyawan ta dauki lamarin korar tawagar Isra'ila daga taron kungiyar tarayyar Afrika da muhimmanci.

 

4122910

 

 

captcha