IQNA

An kama wani da ya yi yunkurin kona wani masallaci a Jamus

17:31 - May 11, 2023
Lambar Labari: 3489126
Tehran (IQNA) 'Yan sandan Jamus sun sanar da cafke wani mutum da ya yi yunkurin cinna wuta a wani masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ghad cewa, kakakin rundunar 'yan sandan kasar Jamus ya bayyana cewa: Wani mutum da 'yan sanda suka san shi ya zuba fetur a gaban wani masallaci a birnin Dresden da ke kudu maso gabashin kasar da yammacin jiya Talata, inda ya yi kokarin cinna masa wuta.

An kama wannan mutum mai shekaru 34 kuma yana karkashin binciken 'yan sanda kan kone-kone. Har yanzu ba a san dalilinsa ba.

An bayyana cewa, wanda ake zargin ya kona kur’ani a wani masallaci a watan Afrilu.

Shaidu sun kira jami’an agajin gaggawa bayan ganin mutumin yana zuba mai a wajen masallacin, wanda a lokacin ya cika da cunkoson jama’a.

 

4140140

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallaci yunkuri kona jamus cunkoso
captcha