IQNA

Domin Fuskantar Ayyukan ‘Yan takfiriyya Ya Kamata A Kafa Kwamitin Malamai

22:29 - November 24, 2014
Lambar Labari: 2611415
Bnagaren kasa da kasa, daya daga cikin mahalarta taron yaki da akidar kafirta musulmi da aka kamala yau a birnin Qom ya yi kira da akafa wani kwamiti na malamai da zai bin kadun hanyoyin yaki da akidar takfiriyya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Abul-aza’im wani daga cikin mahalarta taron yaki da akidar kafirta musulmi da aka kamala yau a birnin Qom na jamhuriyar muslunci ya yi kira da a kafa wani kwamiti na musamman wanda zai kunshi malamai da zai bin kadun hanyoyin yaki da akidar takfiriyya wadda ta zama babbar masifa ga al’umma.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa yau malamin wanda ya zo daga kasar Masar ya bayyana cewa bisa la’akarin da hadarin da wannan mummunar akida take da shi, ya zama wajibi a kafa wani kwamiti wanda zai kunshi malamai ne da kuma masana wadanda za su tattaunawa hanyoyin da za a bi domin yaki da wannan babbar musifa a cikin kasashen musulmi.
Ya kara da cewa hanyar fito na fito da su day ace daga cikin wadannan matakai, amma kuma hakan lamari ne da yashafi gwamnatoci, amma malamai da kuma masana aikinsu shi ne yin amfani da hanyoyi na fadakarwa da jan hankalin matasa da ake rudarsu tare da wanke musu kwakwale domin aikata ta’addanci da sunan jihadi a cikin addinin muslunci.
Wannan shawar ta samu karbuwa daga mafi yawan maalarta taron, wadands uke ganin cewa babban tushen matasalr ma shi ne akidar ta wahabiyanci wadda it ace ke dauke da mahanga ta kafirta sauran musulmi baki daya .
2611386

Abubuwan Da Ya Shafa: qom
captcha