IQNA

Taron Ghadir A London Da Hamburg

22:54 - September 08, 2017
Lambar Labari: 3481875
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar idin Ghadir za a gudanar taruka a cibiyoyon mulsunci na London da kuma Hamburg.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamar yadda aka saba akowace shekara a lokacin zagayowar lokacin idin Ghadir, cibiyar muslunci da ke London a kasar Birtanitya za ta shirya taro da kimanin karfe 18:00 agogon kasar.

Hojjatol Islam Muhammad Ali Shemali da kuma Hajj Behzad Maulayi za su gabatar da jawabi da kuma bege ga shugaban muminai, wanda Allah madsaukakin sarki ya cika ni’imar addinin musulunci da wilayarsa a matsayin ci gaban jagorancin manzon Allah tsira da amincin llah su tabbata a gare shi da alayensa.

Haka nan kuma za a yi wani taron makamancin hakan a birnin Hamburg na kasar Jamus, wanda shi a zai samu halartar mumunai daga koina a cikin birnin har ma da wasu biranan, da kimanin karfe 18:15 a gogon kasar.

Ayatollah Ramezani shi ne babban limamanin masallacin Hamburg kuma shugaban cibiyar muslunci ta birnin, wanda kuma shi ne zai gabatar da jawabi a taron na gobe.

3639620


captcha