Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai Sadal Balad cewa, a wata tattaunawa da ta gudana tsakanin Ahmad Tayyib babban malamin Azhar da kuma jakadan Birtaniya a Masar Jefry Adams a jiya, malamin ya jaddada wajabcin fadada tattaunawa tsakanin mabiya addinan musulunci da kiristanci a duniya.
Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, kara samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinain musulunci da kiristanci a duniya, yana da gagarumin tasiri wajen ci gaban duniya da ma zaman lafiya.
Ya ce a kwanakin bayan sun tattauna wannan batu tare da paparoma, kuma sun cimma matsaya kan yin dukkanin kokari tsakanin fadar Vatican da kuma cibiyar Azahar domin kaiwa ga wannan manufa, kuma bangarorin biyu suna ci gaba da tuntubar juna.
Shi ma a nasa bangaren jakadan na Birtaniya a Masar ya bayyana gamsuwar kasarsa da wannan mataki.