IQNA

Gargadi Kan Karuwar Kyamar Musulmi A Nahiyar Turai

23:33 - February 28, 2020
Lambar Labari: 3484568
Tehran (IQNA) kwamitin yaki da nuna wariya na kasashen turai ya yi gargadi kan karuwar nuna kyama ga musulmi a cikin kasashen nahiyar turai.

Shafin menara.ma ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani rahoto da kwamitin yaki da nuna wariya da ke karkashin babban kwamitin kasashen ya fitar, an bayyana karuwar nuna kyama ga musulmi a cikin kasashen nahiyar turai a halin da cewa shi ne mafi muni.

MariaPeshkinovich ita ce shugabar babban kwamitin kasashen turai, ta bayyana cewa, batu na gaskiya kan cewa nuna kin jinin musulmi a cikin kasashen turai yana kara muni.

Ta ce wannan abin kunya ne mai mai matukar muni, wanda yake kara yaduwa sakamakon maganganu da ake yadawa a cikin kafofin sadarwa na zamani.

Ta kara da cewa dole ne a kawo karshen wannan mummunan dabi’a ta kin jin musulmi a nahiyar turai baki daya, domin wannan ya yi hannun riga da dimukradiyya.

Kwamitin kasashen turai ko kuma (Council of Europe) shi ne kwamiti ko kungiya mafi jimawa da ta hada dukkanin kasashen turai, wadda aka kafa ta tun a cikin shekara ta 1949, wadda dukkanin kasashe 47 suke da mambobi a  cikinta.

 

3881958

 

 

captcha