IQNA

Wasu Manyan Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Ziyarci Sudan Tare Da Ganawa Da Sojojin Kasar

17:38 - January 20, 2022
Lambar Labari: 3486846
Tehran (IQNA) Tashar talabijin ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, wata tawagar yahudawan sahayoniya ta yi tattaki zuwa Sudan domin ganawa da Abdel Fattah al-Burhan, shugaban majalisar gudanarwar kasar da kuma manyan hafsoshin soji.

Tashar Aljazeera ta bayar nata rahoton da ke ishara da cewa, Majiyar sojan Sudan ta tabbatar da cewa wata tawagar tsaro daga gwamnatin Isra’ila ta isa birnin Khartoum domin ganawa da Janar Abdul Rahim Hamdan Daqlu, mataimakin kwamandan dakarun ayyukan gaggawa wanda ya tarbi tawagar.

Har ila yau kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta tabbatar da labarin ziyarar tawagar ta Isra'ila a Sudan, ba tare da bata lokaci ba, sai dai ba ta bayar da cikakken bayani kan hakikanin abin da suka yi a Sudan ba.

Jirgin na tawagar Isra'ila ya tsaya a birnin Sharm el-Sheikh kafin ya shiga birnin Khartoum, inda ya kara da cewa tawagar za ta koma birnin Tel Aviv a daren yau.

A watan Nuwamban da ya gabata, wata tawaga ta yahudawan Isra’ila a hukumance ta ziyarci kasar Sudan, kuma shafin yanar gizo na Axius na Amurka ya ruwaito a lokacin cewa, gwamnatin shugaba Joe Biden ta bukaci gwamnatin Isra’ila da ta yi amfani da alaka ta kut da kut tare da jagoran juyin mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan.

 

 

4029952

 

captcha