IQNA

Yaro dan shekara 4 yana karantar da al-Qur'ani ga ‘yar shekara 3

18:20 - October 14, 2022
Lambar Labari: 3488009
Tehran (IQNA) an faifan bidiyo da ke nuna wani yaro dan shekara hudu yana gyara karatun kur’ani ga kanwarsa ya samu yabo daga masu amfani da shafukan intanet.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tawassul cewa, sha’awar iyali ga kur’ani mai tsarki da karantawa da koyan shi yana bayyana ne a kan yara kanana da yara a cikin iyali, domin yaro ya yi koyi da iyayensa wajen sadaukar da kai ga karatun kur’ani da haddar kur’ani.

A kwanakin baya an yada wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta wanda ya nuna wani karamin yaro yana gyara karatun al-qur'ani ga kanwarsa.

A cikin wannan faifan bidiyon an nuna wata yarinya 'yar shekara uku tana karatun ayoyi a cikin suratul Shams yayin da dan uwanta wanda bai wuce shekara hudu ba ya gyara karatun ta.

Wannan faifan bidiyo ya sami dubban masu kallon a  Twitter.

4091399

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yaro yarinya kanwa shekara ayoyi
captcha