IQNA

An fara rijistan sunayen masu sha'awar shiga horo na koyon ilimin kur'ani a Hamburg

21:06 - May 06, 2023
Lambar Labari: 3489098
Tehran (IQNA) An fara gudanar da rijistan sunayen masu sha’war koyon karatun kur’ani mai tsarki a cibiyar musulunci ta Hamburg.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar Darul kur’ani da ke Hamburg tana shirya darussa na koyar kur’ani mai tsarki da ilmomi da suka shafi kur’ani a kowace ranar Asabar.

An sanya ranar 14 ga watan mayu na wannan shekara ta 2023 a matsayin wa’adin karshe na yin rijistar, ga wadanda suke da shawa’a za su iya tuntuba ta hanyar kafar sada zumunta ta whatsapp a wannan lamba:  00494022948648.

Cibiyar Darul Kur’ani ta kasar Jamus da ke karkashin cibiyar muslunci ta Imam Ali da ke Hamburg, tana gudanar da aikace-aikace n addini a kafofin sada zumunta da kuma shafukan yanar gizo domin amfanin musulmi.

 

4138761

 

 

captcha