IQNA

Al-Azhar Ta Yi Godiya Ga Shugaba Putin Na Rasha Kan Mutunta Kur’ani Mai Tsarki

16:25 - June 30, 2023
Lambar Labari: 3489397
Alkahira (IQNA) A cikin wata sanarwa da ta fitar, babbar cibiyar musulunci ta Al-Azhar da ke Masar ta yaba da matakin da shugaba Vladimir Putin na Rasha ya dauka na mutunta kur'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na  tashar Rasha Al-Yum cewa, 

a cikin wata sanarwa da cibiyar Azhar ta fitar ta bayyana cewa: Al-Azhar na girmama wannan jajirtaccen matsayi na Vladimir Putin wanda ya dauki kur'ani mai tsarki da kare al'amura masu tsarki na musulmi tare da nuna mutunta addinin musulunci.

A lokacin da yake karbar kwafin kur'ani a matsayin kyauta a birnin Darband na kasar Rasha, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi Allah wadai da matakin kona kur'ani mai tsarki tare da daukar wannan mu'amala da littafin musulmi a matsayin babban laifi.

 A yayin ziyarar da ya kai a masallacin Juma'a na Darband, shugaban kasar Rasha ya bayyana cewa: "Jagoran kiristoci na  Rasha a ko da yaushe yana tabbatar mana da cewa musulmi 'yan uwanmu ne kuma duk abin da ya shafe su ya shafe mu ma."

 Ya kara da cewa: Hakan zai karfafa hadin kan al'ummarmu. Kasarmu kasa ce da ta kunshi bangarori daban-daban, amma al'umma daya ce. Wannan littafi mai tsarki ne ga musulmi kuma yana da tsarki da girma ga wasu ma wadanda ba musulmi ba.

Mun san cewa a wasu kasashe suna nuna hali daban, wasu kuma ba sa mutunta addinin mutane, suna cewa wannan ba laifi ba ne.

 Ya ce: "Kona kur'ani a kasarmu ana daukarsa a matsayin bababn laifi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada a cikin sashe na 282 na kundin hukunta laifuka na kasar Rasha.

Wannan na zuwa  a daidai lokacin da  aka kona kur’ani mai tsarki a  kasar Sweden tare da bayar da izinin yin hakan daga hukumomin kasar a matsayin ‘yancin bayyana ra’ayi.

 

 

 

4151372

 

captcha