IQNA

Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya yi watsi da dokar hana sanya hijabi a gasar Olympics ta Paris

15:40 - October 01, 2023
Lambar Labari: 3489905
Kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya yi watsi da matakin da ma'aikatar wasanni ta Faransa ta dauka a baya-bayan nan game da haramta sanya hijabi ga 'yan wasan kasar tare da jaddada cewa dukkan 'yan wasa za su iya shiga kauyen wasannin ba tare da takura ba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khalij Online cewa, kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya bayyana rashin amincewarsa da shirin haramta sanya hijabi a gasar Olympics.

Kwamitin ya bayyana adawarsa bayan ministan wasanni na Faransa ya bayyana cewa za a haramta sanya hijabi a gasar Olympics ta 2024 don mutunta tsarin addini.

Dangane da haka, kakakin kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya ce: Ba za a aiwatar da wannan shawarar ba a gasar Olympics ta 2024. Dokokin kwamitin Olympics na kasa da kasa sun shafi kauyen Olympics, kuma babu wani takunkumi kan hijabi ko tufafin addini da na al'adu. Ana amfani da ƙa'idodin da aka tsara a cikin ƙungiyar ƙasa da ƙasa masu dacewa.

Matakin da Faransa ta dauka na hana 'yan wasanta sanya hijabi ya kuma fuskanci suka daga hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya.

Yayin da kungiyar mata musulmi da aka fi sani da ''masu lullubi'' a Faransa ke kalubalantar sahihancin doka ta 1 na dokokin hukumar kwallon kafa ta Faransa, kasar ta haramta sanya duk wani alamu ko tufafi tun daga shekarar 2016.

Faransa za ta karbi bakuncin gasar Olympics ta bazara daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga Agusta na shekara mai zuwa.

 

4172220

 

captcha