IQNA

Wani yaro dan kasar Bangladesh mai shekaru takwas ya nuna hazaka wajen haddar Alkur'ani

17:41 - December 01, 2023
Lambar Labari: 3490239
Wani yaro dan shekara takwas dan kasar Bangladesh ya samu nasarar haddace kur’ani mai tsarki a cikin kankanin lokaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Bangladesh cewa, wani yaro mai suna Abdullah Al-Fahim mai shekaru takwas a duniya ya samu nasarar haddar kur’ani mai tsarki cikin kwanaki 105.

Ya nuna hazakarsa ne ta hanyar halartar gasar haddar kur'ani mai tsarki ta kasar Bangladesh da aka gudanar a Masallacin Jame Nemat Noor da ke Chattogram.

Fahim shine babban yaro a gidan kuma yana da kanne biyu da kanwa daya. Shi dalibi ne a cibiyar haddar Al-Qur'ani mai suna Hidayat al-Noor kuma yana shirin zama malamin addinin musulunci. Mahaifinsa Salimullah Jahangir limamin wani masallaci a Ukhia a gundumar Chattogram ta kasar Bangladesh.

Hafez Shoaib-ul-Islam Sohail, malamin wannan yaro Hafez, ya ce wannan yaro mai hazaka ya haddace Al-Qur'ani baki daya cikin wata uku da rabi kacal, ina rokon kowa da kowa ya yi masa addu'a.

Fahim ya kuma bayyana farin cikinsa da halartar gasar kur'ani mafi girma a kasarsa inda ya ce yana fatan ya ci gaba da bin tafarkin mahaifinsa na yada addinin Musulunci.

 

4184936

 

captcha