Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin da aka sari Imam Ali (a.s) a bagiren ibada da kuma daren farko na lailatul kadari a ranar 19 ga watan Ramadan mai alfarma, hubbaren Alawi mai tsarki ya karbi bakuncin Masoyan Ahlul Baiti da masun ziyara wadanda suka yi makoki, kuma a daren farko na lailatul kadari suka yi karatun kur'ani da karatun addu’oi na musamman a wannan dare.