IQNA

Miliyoyin masu ziyara a hubbaren Imam Ali (a.s.) a daren shahadarsa

16:45 - April 01, 2024
Lambar Labari: 3490904
IQNA - Haramin Imam Ali (AS) da ke Najaf Ashraf ya shaida halartar miliyoyin masu ziyara daga ko'ina cikin kasar Iraki da kuma kasashe daban-daban a daren shahadarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Alawi cewa, haramin Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf  ya samu halartar miliyoyin maziyarta da suka fito daga sassa daban-daban na kasar Iraki da sauran kasashe daban-daban zuwa wannan wuri mai albarka a dare na biyu na lailatul kadari tare da shahadar wannan Imami mai daraja.

Masu ziyara a hubbaren a daren shahadar Imam Ali (a.s) sun gudanar da ibada da juyayin shahadarsa.

Dangane da haka, masu aikin sa kai kimanin 2,000 sun hada karfi da karfe don samar da yanayi na tsaro, da kuma raba abinci ga masu ziyara.

Har ila yau, tare da hadin gwiwa da hukumomin tsaro da lafiya da na kananan hukumomi na Najaf, hukumar kula da haramin Imam Ali (AS) ta yi kokari na musamman wajen yi wa maziyarta hidima ta fuskar karbar baki da sufuri.

 

 

4207942

 

 

 

captcha