IQNA

An gudanar da tarukan ranar Qudus a kasashe daban-daban na duniya

14:17 - April 06, 2024
Lambar Labari: 3490938
IQNA - An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da kuma yin Allah wadai da laifukan gwamnatin sahyoniyawan a birane daban-daban na duniya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al Arabi cewa, a garuruwa daban-daban na duniya ciki har da kasar Indonesia, an gudanar da jerin gwano na nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu da kuma yin Allah wadai da laifukan gwamnatin sahyoniyawan.

A gefe guda kuma, Tasnim ya rubuta cewa: A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, an gudanar da wani gagarumin tattaki a kasar Malaysia inda mahalarta wannan tattakin suka bayyana hadin kai da al'ummar Palastinu.

Kasancewar al'ummar Kashmir na Pakistan a tattakin ranar Qudus ta duniya

Dubban jama'a daga yankin Kashmir na Pakistan sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga masallacin Al-Aqsa da al'ummar Gaza a daidai lokacin da ake bikin ranar Qudus ta duniya.

Zanga-zangar Ranar Kudus a sansanin Yarmouk, Syria

An gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya a sansanin Yarmouk na kasar Siriya tare da halartar jama'a tare da taken "Tuffan al-Ahrar".

An gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya a Tanzaniya

A lokaci guda da isar juma'ar karshe ta watan Ramadan da ranar Kudus ta duniya; Dubban al'ummar musulmin kasar Tanzaniya sun gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Dar es Salaam fadar mulkin kasar a daidai lokacin da sauran yankunan duniya suka gudanar da zanga-zanga.

Zanga-zangar kishin al'ummar Jordan a ranar Qudus ta duniya

Al'ummar kasar Jordan sun bayyana goyon bayansu ga al'ummar Gaza inda suka gudanar da zanga-zanga a Amman, babban birnin kasar, tare da rera taken nuna goyon baya ga gwagwarmayar Palasdinawa.

Bikin Ranar Qudus ta Duniya a Bahrain

An gudanar da gagarumin tattaki na ranar Qudus ta duniya a gundumar Al-Draz ta kasar Bahrain bayan sallar Juma'a.

Tattakin da al'ummar Malaysia, Indonesia, Nigeria da Bangladesh suka yi na nuna goyon baya ga Falasdinu

Al'ummar birnin Bandung na kasar Indonesiya, sun taru domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu.

A cikin wani rahoto na musamman, tashar Al-Arabi ta Qatar ta sanar da tattakin da al'ummar Malaysia suka yi a Kuala Lumpur domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da Gaza.

‘Yan Najeriya mazauna jihar Bauchi sun fito kan tituna a ranar Kudus ta duniya domin tallafawa kasar Falasdinu.

An kuma gudanar da taron ranar Qudus ta duniya a Bangladesh kuma jama'a sun halarci wani gangami na nuna goyon baya ga Falasdinu.

 

 

 

 

 

 

 

 

4208831

 

 

 

captcha